Shugaban Renamo, babbar jam'iyyar adawa ta kasar Mozambique, Afonso Dhlakama, ya tabbatar a ranar Alhamis cewa, zai yi rajistan shiga zabubukan kasar masu zuwa. A yayin da yake magana a gidan talabijin ta kasa TVM ta wayar tarho, mista Dhlakama ya bayyana cewa, a wannan shekara ce za'a shirya zabubuka na farko bisa tsarin demokaradiyya a kasar ta Mozambique, domin hukumomin zabe, misalin kwamitin shirya zabe mai zaman kansa (CNE) ya kunshe mambobin jam'iyyun siyasa, har ma da wakilan Renamo da na jma'iyyar demokuradiyar kasar MDM.
Zan yi rajista domin zabe, in ji mista Dhlakama. A yayin da ake tambayarsa ko zai shiga takarar zaben shugaban kasa, mista shugaban Renamo ya bayyana cewa, wannan hurumin jam'iyyarsa ne, idan jam'iyya ta yarda in yi takara to zan shiga takara. (Maman Ada)