in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Amurka sun fara tallafawa neman 'yan matan da aka sace a Najeriya
2014-05-13 10:20:18 cri

Hukumar tsaron Amurka ta Pentagon, ta ce, yanzu haka jami'an sojin Amurka 16 sun fara aikin hadin gwiwa da sauran dakarun dake aikin nemo 'yan matan nan da 'yan Boko Haram suka sace a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin hukumar ta Pentagon Steve Warren, ya shaidawa wani taron manema labaru cewa, dakarun sun kunshi kwararru daga fannonin tsaro da bincike daban daban, suna kuma karkashin gudanarwar sashen harkokin wajen Amurka na ofishin jakadancin kasar dake birnin Abuja, fadar gwanmatin Najeriya.

Ya ce, dakarun za su taimakawa gwamnatin Najeriya a kokarinta na shawo kan matsalar da ake fama da ita yanzu haka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China