Shugaba Mahinda Rajapaksa na Sri Lankan ya bayyana takaicinsa game da sace 'yan matan nan su sama da 200, da 'yan Boko Haram suka yi a jihar Bornon Najeriya.
Cikin wata wasikar jaje da ya aike ga shugaban tarayyar Najeriya, shugaba Rajapaksa, ya ce, wannan lamari ya tada hankulan daukacin al'ummar duniya, ya kuma yi kama da irin matakin da 'yan tawayen Tamil Tiger suka taba dauka a Sri Lanka, na tilasawa yara kanana daukar makamai domin yakar gwamnati.
Har ila yau, Mr. Rajapaksa ya bayyana sace 'yan matan a matsayin wani mummunan aikin ta'addanci, wanda ya wajaba a hukunta wadanda suka aikata shi.
Bugu da kari shugaban kasar ta Sri Lanka, ya ce, wannan laifi ya nuna matukar bukatar da ake da ita, ta daukar matakan yaki da ta'addanci daga dukkanin fannoni a kuma daukacin sassan duniya. (Saminu)