in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi tir da barkewar fadace-fadace a kusa da sansanoninta dake Sudan ta Kudu
2014-04-23 10:57:27 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Sudan ta Kudu UNIMISS, ta yi kakkausan suka game da barkewar fadace-fadace a wuraren dake kusa da sansanoninta, lamarin da ya haifar da hauhawar adadin mutanen dake neman mafaka.

A cewar kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric, tashe-tashen hankulan da aka fuskanta a baya bayan nan, sun sanya karuwar wadanda ke samun mafaka a sansanin Bentiu na jihar Unity, kaiwa ga mutane 22,000, daga adadin da bai wuce 4,500 ba a farkon wannan wata na Afirilu da muke ciki.

Wata kididdiga ta MDD ta nuna cewa, ya zuwa yanzu akwai jimillar 'yan gudun hijira 75,000 dake samun mafaka a sansanonin MDD dake sassan kasar daban daban. Don haka ne Dujarric ya nanata muhimmancin baiwa wadannan sansanoni kariyar da ta dace.

Dauki ba dadi tsakanin dakarun gwamnati, da masu goyon bayan tsohon shugaban kasar Riek Machar da ya barke cikin watan Disambar bara ne dai, ya rikide zuwa fadan kabilanci, wanda a cikin watanni biyun da suka gabata ya sabbaba kisan dubban fararen hula a kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China