in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun raya Sin da Afrika na fatan kara zuba jari a Afrika
2013-12-03 10:38:39 cri

Asusun raya Sin da Afrika (CADFund) wanda yanzu haka ya riga ya zuba jari a ayyukan cigaba guda 70 a nahiyar Afrika yana kawo ayyukan zuba jari cikin sauri.

Da yake magana a lokacin wani taro na hauhawar da aka samu a kasuwannin Afrika a ranar Litinin din nan 2 ga wata a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, Wang Yong, mataimakin shugaban asusun ya lura cewa, ya zuwa yanzu, asusun ya riga ya zuba jari a ayyuka 72 a cikin kasashe 30.

Mr. Wang ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, manyan ayyukan da asusun ya rigaya ya zuba jari a ciki sun hada da ayyukan kira, ababen more rayuwa, bangaren aikin noma, cibiyoyin masana'antu da na raya albarkatan hallitu.

Shi dai taron na kwanaki biyu, an shirya shi ne domin manyan 'yan kasuwa da masu zuba jari dake neman hanyoyin da za su fahimci yadda za su shawo kan duk wata matsala da za su fuskanta a lokacin da suka zuba jari a tattalin arzikin nahiyar dake tasowa, tare da yadda za su isar da ayyukansu ga wadanda ake bukata, kamar 'yan kasuwa da masu tsara doka, da zummar ciyar da nahiyar gaba kamar yadda masu shirya taron suka yi bayani.

Alasdair Ross, babban masanin tattalin arziki kuma daya daga cikin shugabannin shirya taron ya shaida wa manema labarai cewa, Sin tana cikin manyan masu taka rawa a duniya, da ma nahiyar Afrika, kuma tana da babbar rawa da take takawa wajen bayar da kwarin gwiwwa na kudaden zuba jari, sai dai kuma duk da hakan ita ma tana samun dama mai kyau wajen zuba jari a ayyukan cigaba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China