in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wadanda suka rasa rayuka a wani hari a karshen mako a Nigerya sun kai 119
2014-03-19 12:15:52 cri

Yawan adadin wadanda suka rasa rayukansu, a wani hari da aka kai jihar Kaduna, wacce ke arewa maso yammacin Nigeriya a yanzu ya kai mutane 119. A jiya Talata, adadin ya karu daga 114, da gwamnatin jihar ta ba da rahoton rasa rayukansu tun farko.

Hukumar samar da agaji na gaggawa ta jihar Kaduna SEMA ta shaidawa 'yan jarida a babban birnin jihar a Kaduna cewar, ta kuma samu adadin jama'a har dubu biyu, wadanda harin ya sa suka rasa muhallansu. Harin dai an kaddamar da shi ne a kauyuka ukku a yankin karamar hukuma ta Kaura dake jihar a karshen makon da ya gabata.

Wakilin hukumar ta SEMA, ya ce, wadanda suka rasa muhallan nasu tuni hukumar bayar da agajin na gaggawa ta samar masu wurin zama, a wata makarantar firamare dake yankin kuma ta ce, a wannan makon ne za ta rarraba masu kayayyakin agaji.

Hukumomi na 'yan sanda a ranar Lahadi sun bayar da umurni na farautar wadanda ake zargi da kashe mutanen kauyukan tare da yin alkawarin kame wadanda ke da hannu wajen aiwatar da harin.

Kakakin 'yan sandan jihar Kaduna, Aminu Lawan ya ce, jami'an tsaro suna tsaye a kan lamarin, kuma an kara tura karin 'yan sanda zuwa wuraren da abin ya shafa. Kakakin ya ce, an baiwa 'yan sandan umurni na tabbatar da doka da oda a yankunan.

Gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Yero, ya kadddamar da cikakken bincike a game da harin da aka kai. Gwamnan ya yi allah wadai da harin da kakkausar murya a inda ya misalta harin da cewar, ba wani abu ba ne illa mugunta da rashin tsoron Allah. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China