in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar likitocin Belgium ta isa Najeriya domin taimakawa iyalan 'yan matan da aka sace
2014-05-12 10:13:24 cri

Kasar Belgium ta dauki niyyar tura a ranar Lahadi da wata tawaga a tarayyar Najeriya domin taimakawa iyalan 'yan matan garin Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace.

Tawagar za ta kwashe kwanaki uku zuwa hudu, kuma za ta yi amfani da wannan lokaci wajen ba da taimakon jinya da ba da kulawa ga iyalan 'yan matan da kungiyar Boko ta sace, da kuma ba da kulawa ga sauran 'yan matan idan aka sako su.

Bisa sakamakon wannan tawagar gani da ido, kasar Belgium za ta dauki matakin tura wata tawagar zaman kanta, ko ba da shawara ko kuma tallafawa wani shirin tarayyar Turai kan wannan batu.

Kwamitin tsaro na MDD ya yi allawadai a ranar Jumma'a da sace 'yan matan da sauran hare-haren ta'addancin baya bayan nan na kungiyar Boko Haram a Najeriya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China