Asusun yara na MDD UNICEF, ya bayyana a ranar Talata 5 ga watan nan cewa, daga watan Afrilun shekarar bara kawo yanzu, kimanin mutane 60 sun gamu da hadarin tashin ragowar ababan fashewa da aka binne a yankunan kasar Mali, inda kuma kashi biyu bisa uku na wannan adadi yara kanana ne.
Bisa kididdiga, a cewar mataimakin kakakin MDD Eduardo del Buey, kimanin yara kanana 200,000 ne dake yankin tsakiya da na arewacin kasar ta Mali ke fuskantar hadarin mutuwa ko samun raunuka, sakamakon ababen fashewa dake binne a sassan yankunan kasar daban-daban. Del Buey wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labaru na rana rana da ya gudanar, ya kara da cewa, yawan wadanda ke fuskantar wannan matsala na iya karuwa, da zarar al'ummomin da suka gujewa gidajensu sun fara komawa yankunan da rikicin kasar ya fi tsamari.(Saminu)