Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta yi kiran da a gudanar da aikin kidaya kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar Madagascar da ya gudana ranar Jumma'a 25 ga wata cikin zaman lafiya, inda ta bukaci 'yan takara 33 da ke neman wannan mukami da su nuna halin sanin ya kamata yayin da suke jiran sakamakon zaben.
Shugaban tawagar masu sa ido na kungiyar, Issaga Kampo ne ya yi wannan kiran yayin taron manema labarai, yana mai cewa, kamata ya yi 'yan takara su guji kalaman batanci da tunzura jama'a.
Kungiyar AU dai ta tura masu sa ido guda 71 a zaben na Madagascar ne, kuma ta nuna yatsa kan matsalolin katunan zabe, da yadda aka gudanar da yakin neman zaben a zagaye na farko na zaben shugaban kasar.
A halin da ke ciki kuma, cibiyar kula da harkokin zabe ta kasar Afirka ta Kudu (EISA) wadda ta tura masu sa ido 20 a zaben kasar ta Madagascar na ranar Jumma'a, ta yi kiran cewa, kamata ya yi ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Madagascar ta ci gaba da rabawa 'yan kasar katin shaidar dan kasa, ta yadda za a sa su cikin kundin masu zabe. (Ibrahim)