Mista Afonso Dhlakama, shugaban babbar jam'iyyar adawa wato Renamo ta kasar Mozambique, ya bayyana fatansa na ganin an tabbatar da matakan tsaro domin fita daga inda ya buya, ta yadda zai samu damar zuwa yin rajista domin shiga zabubukan kasar, a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na kasar AIM ya rawaito a ranar Talata.
Mista Dhlakama, a cewarsa, ga dukkan alamu shi ne za'a zabe a matsayin 'dan takara na jam'iyyar Renamo a zaben shugaban kasa mai zuwa, inda aikin yin rajista zai kammala nan da kwanaki bakwai.
Ba mu tattauna kan kome ba game da dukkan zabubukan, amma ina tsammanin cewa, ko wane 'dan kasar Mozambique yana bukatar samun tsaro domin ya samu damar zuwa yin rajista a matsayin 'dan takara ko a matsayin mai zabe, in ji Saimone Macuiane, wani babban wakilin Renamo a cikin hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AIM. (Maman Ada)