in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin BOAD ya kebe Sefa biliyan 25 zuwa ayyukan cigaba biyu a Nijar
2014-05-13 10:31:00 cri

Bankin cigaban kasashen yammacin Afrika (BOAD) ya baiwa gwamnatin Nijar wani rancen kudi na Sefa biliyan 25, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 50 da za su taimaka wajen gine-ginen hanyoyi da kuma farfado da muhallin hallitu, in ji hukumar kudin a ranar Litinin a cibiyarta dake birnin Lome na kasar Togo.

Yarjejeniyar ba da rancen kudin, an sanya hannu kan ta tsakanin shugaban bankin BOAD, mista Christian Adovelande da ministan fasalin kasa da cigaban karkaran Nijar, Amadou Boubacar Cisse.

A cewar sanarwar bankin, an kebe Sefa biliyan 15 domin gina mahadar Diori Hamani kan hanyar "Independence" da gyaran yankin kasuwar Katako dake birnin Yamai, a yayin da Sefa biliyan 10 suka kasance cikon rancen kudin na ajin farko da ya shafi shirin Kandadji na farfado da muhallin halittu da kulawa da yankin noma na "kwazazzabin Nijar" bisa shirin da zai taimaka wajen rage talauci, kyautata tsaron abinci da kare muhalli ta hanyar farfado da wuraren muhallin halittu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China