Babbar jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya ta ce, ta yi maraba da tayin da Sin da sauran kasashen duniya suka yi na taimaka wa Najeriya wajen gano 'yan mata 'yan makarantan nan da kungiyar Boko Haram ta sace ranar 14 ga watan Afrilun da ya gabata a garin Chibok da ke jihar Borno a tarayyar Najeriya.
Shugaban jam'iyyar na riko Bisi Akande ne ya bayyana hakan ga taron manema labarai a Lagos, inda ya ce, wannan mataki da sauran kasashe da kungiyoyin suka nuna na taimakawa kasar ta Najeriya, ya tabbatar da imanin jam'iyyar cewa, yaki da ayyukan ta'addanci, batu ne na duniya baki daya da ke bukatar hadin kan kowa da kowa.
Shi ma firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya baiwa shugaban Najeriya tabbaci a lokacin da ya kai ziyarar aiki kasar cewa, kasar Sin za ta taimaka wa kokarin kasar na yaki da ayyukan ta'addanci daga dukkan fannoni, ciki har da horas da sojojinta fasahohin yaki da masu tayar da kayar baya.
A yayin tattaunawarsu da shugaba Jonathan, Li Keqiang ya yi alkawarin cewa, kasarsa za ta sanar da kasar ta Najeriya irin bayanan da ta tattara ta tauraron dan-adam dinta da kuma jami'anta na leken asiri. (Ibrahim)