Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya gabatar a ranar Lahadi da shirin karbar wani taron da zai hada Najeriya da kasashen dake makwabtaka da wannan kasa dake yammacin Afrika domin tattauna batun sace 'yan matan da kungiyar Boko Haram ta yi, a wani labarin da kafofin watsa labarai na kasar suka bayar.
Shugaba Hollande ya yi wadannan kalamai a lokacin ziyararsa a Bakou, babban birnin Azerbaijan.
Fiye da 'yan mata 200 na makarantar sakandare dake garin Chibok a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, aka yi awon gaba da su a cikin watan Afrilu, kuma kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin sace su tare da barazanar sayar da 'yan matan. (Maman Ada)