in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Belgium ta yi allawadai da tashin hankalin ta'addanci a Najeriya
2014-05-09 11:16:51 cri

Mataimakin faraminista kuma ministan harkokin wajen kasar Belgium, Didier Reynders, ya kawo bayansa a ranar Alhamis domin yin allawadai da babbar murya kan ayyukan tashe-tashen hankali dake kamari na kashe mutane da sace mutane dake da hannun 'yan kungiyar Boko Haram.

Mista Reynders ya kira gamayyar kasa da kasa da ta taimakawa hukumomin Najeriya domin kawo karshen wannan babbar matsala.

Rikicin da tuni ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane da kuma kawo ja da baya ga 'yancin matasa wajen samun ilimi da kuma tushen zaman al'umma mai 'yanci, in ji Didier Reynders.

Haka kuma jami'in na nuna yabo game da taimako da goyon bayan da gamayyar kasa da kasa take nuna wa al'ummar Najeriya da kuma yaba wa da taimakon da kasashen suke shirin baiwa Najeriya a wannan fanni. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China