in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin faraministan Somiliya na ziyarar aiki a Djibouti
2014-04-15 09:22:12 cri

Mataimakin faraministan kasar Somaliya Ridwan Hersi Mohamed ya kai wata ziyarar aiki a kasar Djibouti dake makwabtaka da kasarsa tun ranar Asabar, kuma ya samu ganawa a ranar Litinin tare da shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh.

Bayan wannan ganawa, mataimakin faraministan Somaliya ya shaidawa manema labarai cewa, ya yi amfani da wannan ziyara domin bayyana yabo da godiyar gwamnatinsa da na al'ummar kasarsa game da kokarin da kasar Djibouti ke yi domin shimfida zaman lafiya da kuma sake gina kasar Somaliya.

Hersi Mohamed ya nuna jin dadinsa game da matakin da hukumomin Djibouti suka dauka na kara tura wata rundunar sojoji a karo na biyu a kasar Somaliya.

A yayin wannan ziyara, bangarorin biyu sun dauki niyyar kara ingiza da karasa yarjejeniyoyin hadin gwiwar al'adu dake da manufar bunkasa musanyar kwarewa a fannonin horar da masu fasaha, furdusan wasannin al'adu da na fina finai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China