Sace 'yan matan da aka yi baya bayan nan a yankin arewa maso gabashin Najeriya na bayyana kawo karshen ta'addanci a cikin wannan kasa dake yammacin Afrika, in ji shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan a ranar Alhamis.
Mista Jonathan ya yi wannan furuci a cikin wani jawabin da ya gabatar a yayin dandalin tattalin arzikin duniya kan Afrika.
A cikin wata hira ta musamman tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, shugaban Najeriya ya bayyana cewa, nan da dan lokaci kalilan, gwamnati za ta dage rudanin dake kewaye da sace wadannan 'yan mata, musamman tare da taimakon kasashen waje, da kuma zuba jari a Najeriya da tuni kasar Najeriya ta fara samu tun lokacin da wannan hadari ya faru a tsakiyar watan Afrilu.
Mista Jonathan ya yi imanin cewa, ta'addanci ba zai hana cigaban tsarin mulki na gari ba a cikin kasarsa dake shiyyar yammacin Afrika, a nahiyar Afrika ko a sauran kasashen duniya.
Ta'addanci na daya daga cikin manyan kalubalolin tsaro da ake fuskanta yanzu a Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a Afrika, in ji shugaban Najeriya. (Maman Ada)