Babban sakatare na MDD, mista Ban Ki-moon ya bayyana fargabarsa kan halin da 'yan matan da aka sace baya bayan nan a jihar bornon Najeriya suke ciki, a yayin wata hira ta wayar tarho tare da shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan, in ji kakakinsa a cikin wata sanarwa zuwa ga manema labarai.
Mista Ban ya nuna fahimtarsa kan tashin hankalin da iyalan wadannan 'yan mata suke ciki, da ma kuma al'ummar Najeriya a cikin wannan yanayi na kaduwa, tare da kara jaddada cewa, sake kai irin wannan hari kan yara da makarantu na sabawa dokokin kasa da kasa, kuma abu ne da babu hujjar yinsa ta ko wane hali, in ji kakakin mista Ban.
A yayin hirarsa ta wayar tarho tare da shugaba Jonathan, mista Ban ya bayyana goyon bayansa ga al'ummar Najeriya, musammun ma iyalan wadannan 'yan mata.
Shugaban Najeriya ya sanar da sakatare janar na MDD kan halin da ake ciki game da binciken da ake gudanar domin ceto 'yan matan da aka sace. Haka kuma shugaban Jonathan ya amince da tayin mista Ban Ki-moon na turo da wani babban jami'i a Najeriya domin tattaunawa kan yadda MDD za ta iyar ba da nata taimako wajen tallafawa gwamnatin Najeriya fuskantar kalubalen dake gabanta na cikin gida. (Maman Ada)