in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Birtaniya sun samarwa Najeriya fasahar zamani domin gano 'yan matan da aka sace
2014-05-08 14:47:10 cri

Kasashen Sin da Birtaniya sun samar da fasahohin zamani ga Najeriya domin Nigeria ta samar da wadannan fasahohi ga hukumominta na tsaro, wadanda yanzu haka suna gudanar da wani kokari na ceto 'yan mata da aka sace.

Mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara na musamman a kan al'amurran yada labarai, Reuben Abati ya shaidawa wani taron manema labarai a Abuja, cewar, kasar Sin ta baiwa Najeriya tayin taimakawa wajen gano 'yan matan da aka sace.

A yayin wata tattaunawa da shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan, a farkon safiya yau, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi alkawari cewa, kasarsa za ta baiwa hukumomin tsaro na Najeriya, duk wani muhimman bayanai da ta samu daga tauraron 'dan adam dinta da kuma hukumominta na leken asiri.

A halin da ake ciki, firaministan na kasar Sin, Li Keqiang wanda yanzu haka yake gudanar da wata ziyarar aiki a Najeriya, ya bayar da tabbacin cewar, kasar Sin za ta goyawa Najeriya baya a yakin da take fafutukar yi da ta'addanci ta ko wace hanya, kuma hakan zai hada da taimakawa Najeriya horas da jami'an rundunar sojojin kasar tunkarar hare-hare na 'yan ta'adda.

Reuben Abati ya kuma ce, a sakamakon wani roko da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gabatar masa, firaminstan Britaniya, David Cameron, ya yi alkawarin shigar da kayayyakin neman bayanai na sirri zuwa Najeriya, domin agazawa shirukkan gudanar da ayyukan ganowa da aiwatar da aikin ceto. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China