Rahotanni daga rundunar sojin ruwan Najeriya sun tabbatar da sace wasu Amurkawa su biyu, a wani wuri dake daf da gabar tsibirin Brass a yankin Niger Delta dake kasar. An ce, mutanen biyu da wasu 'yan fashin teku suka sace jami'ai ne na wani jirgin ruwan dakon man wani kamfanin Amurka.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar sojin ruwan Najeriyar Kabiru Aliyu, ya ce, tuni jami'an tsaro suka fara bincike domin ceto Amurkawan biyu.
Wasu rahotanni dai na nuna cewa, ana samun karuwar ayyukan masu fashin teku a yankin na Niger Delta a 'yan kwanakin nan, inda ko da a ranar Talatar da ta gabata ma sai da jami'an rundunar sojin ruwan kasar suka fatattaki wasu 'yan fashin tekun a yankin kogin Odioma, dake daf da tsibirin Brass. Har ila yau a ranar Laraba 23 ga wata, wasu 'yan fashin tekun sun hallaka sojoji biyu, bayan da suka yi musu kwantan bauna a kogin Ikuru dake jihar Rivers. (Saminu)