in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na shirin tura rukunin masu sa ido a zaben Burundi a shekara mai zuwa
2014-02-14 09:47:31 cri

Kwamitin tsaro na MDD ya yanke shawarar nada rukunin masu sa ido game da babban zaben kasar Burundi dake gabashin Afrika a shekara mai zuwa.

A cikin abubuwan da kwamitin ya zartas da su a zamansa na ranar Alhamis, ya ce, ya yi nazarin bukatar da gwamnatin kasar Burundi ta gabatar ta son a aika da rukunin masu lura da zabe na majalissar kafin zaben, lokacin zaben da ma bayan zaben, tare da neman babban magatakardan majalissar ya kafa wannan rukunin.

Haka kuma kwamitin tsaron ya amince da kara wa'adin aikin ofishin majalissar dake Burundi har zuwa 31 ga watan Disambar shekaran nan, sannan ya bukaci manzon musamman na magatakardan MDD ya kammala shirin mika ofishin nan a watan Mayu mai zuwa domin shirin babban zaben kasar.

Kwamitin har ila yau ya yi maraba da amincewar da aka yi da jadawalin zaben na watan Maris din nan mai zuwa tare da kira ga gwamnatin kasar ta Burundi da sauran jam'iyyun siyasan da su tabattar da bin wannan jadawali da shawarwarin da ya gabatar dangane da babban zaben shugaban kasa da na 'yan majalissar wakilai a shekarar ta 2015.

Kwamitin sulhun na MDD mai wakilai 15 ya karfafa wa gwamnatin Burundi gwiwwar inganta kokarin shi na aiwatar da kwaskwarimar da nufin kyautata yanayin siyasa, tattalin arziki da mulki, sannan kuma da magance cin hanci a kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China