in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi suka kan hari da aka kaiwa sansanin MDD a Sudan ta Kudu
2014-04-18 15:00:04 cri

A jiya Alhamis ne, babban sakataren MDD Ban-Ki-moon ya yi tir da wani hari da aka kaiwa sansanin MDD dake Sudan ta Kudu, a inda rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta MDD take bayar da kariya ga fararen hula na kasar.

Wata sanarwa wacce kakakin Ban Ki-Moon ya rarraba ta ce, harin da aka kaiwa fararen hula da rundunar masu kiyaye zaman lafiya a sansanin MDD ta Sudan ta Kudu UNMISS, dake Bor, babban birnin jihar Jonglei, wani abu ne dake nuni da yadda halin rikicin ya tabarbare.

Babban Sakataren MDD ya bukaci gwamnatin ta Sudan ta Kudu da ta dauki matakai nan take, domin tabbatar da tsaron lafiyar rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya, da kuma tabbatar da kariya a wuraren da ake kare fararen hula, a inda kuma ya yi kira a kan dukanin bangarorin dake ga maciji da juna da su dakatar da duk wani mataki ko batutuwa, wadanda ka iya ingiza wutar rikicin da ake fuskanta.

Ban Ki-moon, ya kuma mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda aka kashe 'yan uwansu a yayin da aka kai farmakin, a inda kuma ya yi alkawarin samar da duk goyon bayan da zai yiwu ga wadanda suka jikkata a sakamakon farmakin.

Rahotanni sun ce, an kai harin ne a ranar Alhamis a kan wadansu 'yan tsirarun kabilu, wadanda suka fake a cikin ginin na MDD.

Akalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu a yayin da aka kai farmakin. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China