in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MSF ta kirayi a dakatar da kisa a Sudan ta Kudu
2014-04-29 12:42:25 cri

Kungiyar bayar da taimakon agajin lafiya ta likitoci marasa shinge ta duniya MSF, ta yi kira a kan kungiyoyi masu fada da juna na Sudan ta Kudu da su dakatar da kashe-kashen jama'a domin samun tabbacin halin kwarai na dakarun dake karkashin ikonsu, a inda kungiyar ta kara da cewar, sakamakon tashe-tashen-n hankulan da ake yi, dubannin jama'a sun fada cikin hadari.

A cikin wata sanarwa da kungiyar agajin ta bayar a Nairobi, ta yi tir da mugun tashin hankalin da aka yi a Bentiu a ranar 15 ga watan Aprilu, a inda kungiyar ta bukaci kwamandojin dakarun 'yan tawaye da su kare jama'ar wuraren dake karkashin ikonsu.

Kungiyar ta ce, a sakamakon rikicin daruruwan dubannin jama'a, tilas ta sa sun tsallake matsuguninsu, sun nemi mafaka a sansanonin jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD dake Bentiu domin neman tsira daga tashin hankalin da ake yi.

To amma kungiyar agajin ta likitoci ta ce, wadanda suka nemi mafaka a yanzu haka suna zaune ne a sansanonin a cikin wani halin rashin wurin zama mai kyau, dake barazana ga rayuwar jama'a.

A halin da ake ciki, bayanai da kungiyar agajin ta samu na nuni cewar, ana gudanar da kashe-kashen jama'a wanda ana sane, aka aiwatar da su, wannan ya hada da wani hari da aka kai a asibitin jiha ta Bentiu. wannan wata matashiya ce a game da karuwar jerin tashe-tashen hankula da ake yi Sudan ta kudu.

Kungiyar bayar da taimakon agajin, ta yi gargadi cewar, idan har ba'a magance matsalolin dake fuskantar jama'a dake zamne a irin wadannan sansanoni ba, akwai yiwuwar mutane za su rasa rayukansu a sakamakon matsalar karancin ruwa da tsabta da zaman da ake yi a cakude da juna wanda ka iya haddasa cututtuka wadanda ana iya maganin su.

Kungiyar ta ce, mutanen wadanda suka rasa muhallansu na cikin wani hali na gaba kura baya sayaki, watau ya zaman musu dole su yi zabi tsakanin zama a gidajensu inda babu tabbas na tsaron lafiyarsu, ko kuma zama cikin halin rashin tsabtar wurin zama na sansanonin jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD dake kasar. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China