Ofishin gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Zimbabwe NANGO, ya bukaci kungiyar tarayyar Turai EU, da ta dage takunkumin da ta kakabawa shugaban kasar Robert Mugabe da matarsa.
A hannu guda kuma NANGO ya bukaci gwamnatin Mugabe da ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye, wadanda za su magance takaddamar dake tsakanin fadar gwamnatin kasar da EU.
Wannan dai kira na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin, wadda kuma ta jaddada muhimmancin daukar matakan shawo kan wannan lamari, matakin da sanarwar ta ce, zai ba da damar fuskantar kalubalen cigaban kasar yadda ya kamata.
NANGO ya yabawa matakin dagewa wasu 'yan kasar su 8 takunkumi da EU ta yi a baya bayan nan. Tana mai cewa, abu ne mawuyaci Zimbabwe, ta iya sauke nauyin dake kanta, don gane da batun kare hakkokin bil'adama a matakin kasa da kasa, muddin tana fuskantar wariya daga kasashen duniya. (Saminu)