'Yan jarida dake aiki a tarayyar Najeriya, an yi kiransu da su rika yin hattara kan tsaron lafiyarsu a yayin da suke gudanar da aikinsu kafin zabubukan da za'a gudanar a kasar.
Shugaban kungiyar 'yan jarida ta kasar (NUJ), Deji Olumoye, ya yi wannan gargadi a ranar Lahadi ta hanyar sanar da mambobin kungiyar a yayin taron wata wata na kwamtin NUJ.
Ya gargadi 'yan jaridar da su rika barci a ofisoshinsu idan har akwai hadarin komawa gidajensu a tsakar dare.
Haka kuma, yana da kyau 'yan jarida su rika kauracewa fitar kudi a wasu lokuta a na'urorin fitar da kudi domin kiyaye kansu daga 'yan fashi da makami.
Deji Olumoye ya yi wadannan kalamai ne saboda aka kashe wani editan wata jarida a ranar 31 ga watan Janairun a karkarar birnin Lagos. (Maman Ada)