Wakilan kwamitin tsaron MDD sun fara gudanar da wani taron gaggawa a daren jiya Lahadi, domin tattaunawa kan matsalolin dake addabar gabashin kasar Ukraine, biyowa bayan kwace wata helkwatar 'yan sanda da wasu masu goyon bayan Rasha suka yi a yankin.
Tsakanin watan Fabarairu ya zuwa yanzu dai kwamitin ya kira taruka 10, a yunkurinsa na magance matsalar siyasar dake addabar kasar ta Ukraine. Baya ga yunkurin da babban zaman majalissar ya yi na shiga maganar a ranar 27 ga watan Maris.
Wasu jawabai da aka gabatar yayin zaman na jiya sun nuna cewa, cikin awoyi 24 kadai, akwai a kalla birane 5 da dakaru masu dauke da makamai ke yiwa barazana. Cikin biranen da ke fuskantar irin wannan barazana dai akwai Sloviansk, da Kramatorsk, da kuma birnin Druzhkivka.
Tattaunawar kwamitin tsaron na zuwa a daidai lokacin da mahukuntan Ukraine ke cewa, sun fara daukar matakan yaki da ta'addanci a yankunan gabashin kasar.
A wani ci gaban kuma babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana matukar damuwarsa, game da halin da ake ciki na tabarbarewar yanayin tsaro a gabashin kasar ta Ukraine, yana mai kira ga daukacin sassan da abun ya shafa da su kai zuciya nesa, su kuma guji daukar matakan da ka iya rura wutar rikici. (Saminu)