in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya kama hanyar yin ziyara a kasashen Afirka
2014-05-04 10:03:19 cri
A yau Lahadi 4 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kama hanyar yin ziyara a kasashen Afirka guda hudu da suka kunshi Habasha, , Nijeriya, Angola da kuma Kenya. Ziyarar dai na bisa goron gayyatar da firaministan kasar Habasha Hailemariam Dessalegn da shugaban karba-karba na yanzu na kungiyar tarayyar Afirka wanda kuma shi ne shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz da shugabar hukumar kungiyar tarayyar Afirka Nkosazana Clarice Dlamini-Zuma da shugaban tarayyar Nijeriya Goodluck Jonathan da shugaban kasar Angola José Eduardo dos Santos da ma shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta suka ba shi. Har wa yau kuma, bisa gayyatar da shugaban taron dandalin tattaunawar harkokin tattalin arzikin duniya, Klaus Schwab ya yi masa, Mr.Li Keqiang zai kuma halarci taron kolin Afirka na dandalin da za a gudanar karo na 24 a Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya. (Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China