in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta ce, ziyarar firaministan Sin na da muhimmanci a gabashin Afrika
2014-05-04 10:15:27 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce, ziyarar da firaministan kasar Sin Li Keqiang zai yi a kasarsa tana da muhimmanci ga cigaban yankin gabashin Afrika.

Shugaba Kenyatta wanda ya bayyana hakan a jiya Asabar 3 ga wata lokacin da ya gana da jakadan kasar Sin dake kasar Kenya, Liu Xianfa a Nairobi, ya ce, ziyarar Mr. Li Keqiang, wani babban mataki ne na inganta dangantaka da cigaba a wannan yankin.

A lokacin ganawar, shugaba Kenyatta ya bayyana cewa, yankin na bukatar abokan hulda masu karfi da ba kawai za su goyi bayan shirin tattalin arziki ba, har ma za su taimaka wajen zaman lafiya.

A nasa bangaren, jakadan kasar Sin a Kenya Liu Xianfa ya yi wa shugaba Kenyatta cikakken bayani game da ziyarar firaministan na Sin a nahiyar Afrika, wato zai fara daga kasar Habasha, shi kuma zai ziyarci kasashen Angola da Najeriya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China