140502murtala.m4a
|
Bisa goron gayyatar shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang zai kawo ziyara a tarayyar Najeriya daga ranar 6 zuwa 8 ga watan Mayu, inda zai kuma halarci taron kolin kasashen Afirka na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya wanda za'a yi a Abuja. Sabon jakadan kasar Sin dake Najeriya Mista Gu Xiaojie ya ce, ziyarar Mista Li Keqiang a wannan karo zata kara karfafa dankon zumunci tsakanin Sin da Najeriya.
Ya ce, shekarar da muke ciki, shekara ce ta cika shekaru 50 da tsohon firaministan kasar Sin marigayi Zhou Enlai ya ziyarci nahiyar Afirka a karon farko, kuma ziyarar firaministan kasar Sin Li Keqiang a wannan karo na da muhimmiyar ma'ana.
Jakada Gu Xiaojie ya ce, Najeriya na taka muhimmiyar rawa a nahiyar Afirka, kuma dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya ta samu ci gaba sosai a fannonin da suka shafi siyasa, tattalin arziki, cinikayya, al'adu da sauransu. Mista Gu ya ce, yayin ziyarar Li Keqiang a Najeriya, zai gana da shugaba Goodluck Jonathan, da rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi na fadada hadin-gwiwa. Haka kuma Mista Li zai halarci taron kasashen Afirka na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya, inda zai gabatar da wani muhimmin jawabi.
Jakada Gu Xiaojie ya kara da cewa, shekara ta 2014, shekara ce ta cika shekaru 10 da kafa dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Najeriya, yana fatan kasashen biyu za su yi amfani da wannan dama domin habaka hadin-gwiwa a fannoni daban-daban, da karfafa zumunta tsakanin al'ummarsu, a wani kokarin raya huldodin kasashen Sin da Najeriya gaba.(Murtala)