Firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya ce, kasashen Sin da Habasha suna cin gajiyar dangantaka mai kyau a tsakaninsu.
Hailemariam Desalegn da yake zantawa da wasu manema labarai na kasar Sin a jiya Asabar 3 ga wata a Adiss Ababa, babban birnin kasar, ya yi nuni da cewa, mai da kasar a matsayin zangon farko na ziyarar firaministan kasar Sin Li Keqiang zai kara karfafa dankon zumunci.
Desalegn ya ce, a kwanakin baya ya kai ziyara a kasar Sin, kuma makasudin musanyar wannan ziyara a tsakanin shugabannin shi ne domin kara karfafa zumunci dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce, gudanar da manyan ayyuka na samar da ababen more rayuwa, layukan dogo, makamashi da kere-kere, Sinawa sun taimaka wajen gaggauta cigaban kasar ta Habasha. (Fatimah)