Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan, ya ziyarci tashar motar Nyanya, dake wajen birnin Abuja, babban birnin kasar inda wani abu da ake zaton bam ne ya tarwatse da sanyin safiyar Litinin. Lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla 71, tare da jikkata wasu 124.
Da yake tsokaci don gane da aukuwar lamarin, shugaba Jonathan ya alkawarta daukar kwararan matakan dakile ayyukan ta'addanci, duba da yadda hakan ke ci gaba da kasancewa wani babban kalubalen dake addabar kasar.
Shugaba Jonathan ya kuma ziyarci asibitocin da aka kwantar da wadanda suka jikkata sakamakon fashewar da ta auku. (Saminu)