Babban darektan hukumar kula da abinci ta duniya (WFP) da babban jami'in kula da 'yan gudun hijira na majalisar dunkin duniya (UNHCR) sun kammala ziyarar aikinsu ta kwanaki biyu a kasar Sudan ta Kudu a ranar Talata, inda suka nuna damuwarsu matuka game da yawan bukatun da wannan rikici ya janyo, tare da yin kira da a samar da mafitar gaggawa.
A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa a karshen ziyarar kwanaki ta biyu, babban jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira na MDD, mista Antonio Guterres da darektar zartarwa ta WFP, madam Ertharin Cousin, sun yi gargadin cewa, rikicin kasar Sudan ta Kudu ka iyar janyo hadari ga miliyoyin mutane a tsawon watanni masu zuwa idan ba'a dauki kwararrun matakan gaggawa domin kawo karshen wannan rikici ba, da kuma kai taimako ga fararen hula dake kokarin tsirar da rayuwarsu. (Maman Ada)