in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire ta bukaci a janye mata takunkumi kan cinikin lu'u-lu'u
2013-09-13 15:29:51 cri

Kasar Cote d'Ivoire ta dauki niyyar daukar matakan da suka wajaba domin ganin an janye takunkumin da MDD ta yi mata kan saida lu'u-lu'u tun bayan barkewar matsalar tawaye da ta raba kasar biyu tsakanin shekarar 2002 da ta 2010. Bayan wani zaman taron ministoci na ranar Laraba, gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ta umurni ministanta na masana'antu da ma'adinai da ya dauki duk wasu matakan da suka wajaba da za su taimaka wajen cimma hanyar dage takunkumin MDD kan cinikin lu'u-lu'u da aka zama kasar a shekarar 2005, a cewar sanarwar karshen taron ministocin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kofinta. 'Cimma burin wannan shiri na dage wannan takunkumi na da muhimmaci domin cigaban sana'ar lu'u-lu'u a kasar Cote d'Ivoire.' in ji gwamnati.

A shekarar 2005, bayan wani kudurin MDD, an hana kasashe su yi cinikin lu'u-lu'un dake fito wa daga kasar Cote d'Ivoire. Ana zargin kasar da hakar wannan karfe mai daraja ta barauniyar hanya a yankunan dake hannun tsoffin 'yan tawayen arewacin da kuma shigar da wannan lu'u-lu'u a cikin kasuwannin kasa da kasa.

A cewar kungiyar Ingila mai zamanta ta Global Witness sumugal din lu'u-lu'u ya kasance wani jigon yaki ga tsoffin 'yan tawaye dake iyar hakar kusan Carat dubu dari uku a ko wace shekara. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China