Kungiyar raya gwamnatocin kasashen gabashin Afirka IGAD ta bayyana a ranar Litinin cewa, an fara sabon zagayen shawarwarin zaman lafiya dake da manufar kawo karshen yakin tsawon watannin hudu a kasar Afrika ta Kudu a birnin Addis Abeba na kasar Habasha. Zaman taro na uku na zagaye na biyu na shawarwarin zaman lafiya da aka gusa zuwa ranar 7 ga watan Afrilu zai mai da hankali wajen sassanta 'yan kasa, in ji sanarwar masu shiga tsakani game da batun zaman lafiya a karkashin jagorancin kungiyar IGAD. Haka kuma sanarwar ta kara da cewa, manzonnin musamman na kungiyar IGAD sun yi amfani da lokacin da aka gusa domin gudanar da jerin shawarwari tare da shugabannin bangarorin biyu, wato shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar da ya zama babban abokin gabansa, a cikin wani kokarin gaggauta shirin shawarwari da kuma kaucewa barkewar wani sabon rikici. (Maman Ada)