Akwai haduran abkuwar tashe-tashen hankali masu tsanani a kasar Burundi duk da cewa, sakamakon jarjejeniyar Arusha kan zaman lafiya da sasanta 'yan kasar Burundi (AAPRB) ta watan Agustan shekarar 2000 tana nan, in ji Gerard Nduwayo, mai fashin baki na kasa da kasa game da harkokin shiga tsakani da rigakafin yake-yake a ranar Laraba a birnin Bujumbura da yake magana a yayin wani zaman taro kan makasudin zaman lafiya mai alfanu.
Jami'in ya ce, kasar Burundi na fuskantar muhimman hadura hudu dake iyar janyo tashe-tashen hankali masu tsanani, inda yake ba da misali game da jita-jita da bacin rai kan shirye-shiryen zabubukan da ake jira a shekarar 2015, rashin sanya ido daga wajen hukumomin kasa kan manufofin da 'yan takara da jam'iyyun siyasa suke bi, rashin tattaunawa tsakanin jam'iyyun siyasa da gwamnati, fargabar tashe-tashen hankali dake da nasaba da rikicin filaye da kuma shigar da matasa aikin soja. (Maman Ada)