Wata kotu dake kasar Libya ta kara bude sauraren kara da take yi na wasu gungun manyan jami'an gwamnatin tsohon shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi.
Kotun, wacce ta fara tuhumar mutanen, bayan da ta nuno 'dan Gaddafi Saif al Islam, a cikin wani hoton da aka hada na bidiyo.
Su dai wadanda ake yiwa shari'a suna fuskantar tuhuma ne a kan zargin da ake yi masu na aikata fyade kara zube, tare da ingiza jama'a shiga tashin hankali, tare kuma da yiwa hadin kan kasar ta Libya zagon kasa, a lokacin da ake yakin, wanda ya haifar da rugujewar tsohuwar gwamnatin kasar.
Wasu bayanan hotuna na bidiyon dake fitowa daga kotun dake kudancin Tripoli sun nuno 'dan Gaddafin yana amsa tambayoyin da alkalan kotun suka tambaye shi.
Dan tsohon shugaban kasar ya ce, kotun ta kaucewa tsarin doka a inda ya ce, ba'a ba shi damar mallakar lauya ba domin ya kare kansa.
A halin da ake ciki, 'dan tsohon shugaban kasar ta Libya, Saif al-Islam, yana hannun wasu 'yan bindiga ne dake yammacin birnin Zintan.
Su dai wadannan 'yan bindiga sun ki su mika 'dan Gaddafin zuwa Tripoli haka kawai zikau ba tare da an ba su fansa ba.
An dai dauki kusan awowi ukku ana ta shari'a a kotu, a inda daga nan sai kotun ta dage kara zuwa 11 ga watan Mayu, kotun ta kuma baiwa Saif al-Islam lokaci domin nada lauyan da zai kare shi. (Suwaiba)