Kwamitin da aka dorawa alhakin sake tsara daftarin kundin mulkin kasar Libya ya yi zamansa na farko a ranar Litinin, lamarin da ya shaida bude sabon shafi ga tsarin mulkin kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa, manyan shugabannin al'umma, da wakilan gwamnati, tare da 'yan jaridu da dama ne suka halarci zaman kwamitin na farko, wanda ya gudana a garin Al-Beida, da ke da nisan kilomita 1,200 daga babban birnin kasar Tripoli.
Yayin zaman kwamitin na farko, an tattauna game da wasu shirye-shiryen gudanar da ayyukansa kamar yadda aka tsara. Ana kuma sa ran kammalar aikin da aka dorawa kwamitin cikin kwanaki 120. Kaza lika daftarin dokokin da kwamitin zai fitar ne, za su kasance ginshikin kafa sabuwar gwamnatin kasar ta gaba.
Masu fashin baki dai na ganin mai yiwuwa ne lokacin da aka kebewa kwamitin ya yi kadan.
Libya dai ta tsundamu cikin halin rashin tabbas a siyasance, tare da barkewar tashe-tsahen hankula tsakanin kabilunta sau da dama, tun bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi. (Saminu)