in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru na nuna damuwa kan bacewar harsunan kabilu a Kenya
2014-04-16 09:44:56 cri

Kwararru sun yi kashedi game da ja da baya sannu a kankali kan amfani da harsunan kabilu a kasar Kenya.

A karkashin jagorancin ministan ilimin kasar Kenya, Jacob Kaimenyi, kwararrun sun bayyana cewa, a yanzu ya zama wajibi a bullo da wasu litattafan dake kunshe da rubuce rubucen wadannan harsuna.

Dunkulewar duniya wuri guda ya janyo bunkasar harsunan waje maimakon harsunan gida, in ji mista Kaimenyi a yayin bikin kaddamar da amfanin kamus da tarihin harshen Ekegusii da aka gudana a Litinin 14 ga wata. Wannan kundi ya kunshe fiye da kalmomi dubu 13 bayan tsawon shekaru goma na baya bayan nan na binkice.

Ekegusii, harshe ne na kabilar Kisii dake zama a yankin yammacin kasar Kenya. A yanzu haka kuma Kenya na shirin aiwatar da wata manufa da za ta tilasta amfani da harsunan gida a tsawon farkon shekaru na makaranta. Kasar dake amfani da harsuna da dama ta fi samun cigaba, in ji ministan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China