in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin bam ya hallaka mutane 4 a Nairobin Kenya
2014-04-24 10:09:18 cri

Rahotanni daga birnin Nairobin kasar Kenya, na cewa, wani bam da wasu 'yan kunar bakin wake suka tayar a cikin wata mota, ya hallaka maharan su biyu tare da wasu 'yan sanda biyu, yayin da kuma mutane da dama suka jikkata.

An ce, motar da maharan ke ciki ta tsaya ne daura da caji ofis din 'yan sanda dake Pangani, kuma bam din dake cikinta ya tarwatse yayin da 'yan sandan biyu suka kusanci motar da niyyar tuhumar wadanda ke ciki.

Harin dai na ranar Laraba ya auku ne a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar barazanar tsaro, daga magoya bayan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin Islama dake da alaka da Al-Shabaab da Al-Qaida. Lamarin da ake alakantawa da ramuwar gayyar da Al-Shabaab ta ce tana yi, bisa tallafi da Kenya ta baiwa Somaliya wajen fatattakar mayakanta.

Rundunar 'yan sandan kasar ta Kenya dai ta ce, duk da matakan tsaurara tsaro da ake dauka, akwai babban kalubale, don haka dole al'umma su yi taka tsantsan, domin kare aukuwar karin hare-hare daga dakarun kungiyoyin 'yan fafutika. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China