Kwamitin bincike na kungiyar tarayyar Afrika AU kan kasar Sudan ta Kudu na ziyarar aiki ta farko a kasar ta Sudan ta Kudu tun daga ranar 21 ga watan Afrilu har zuwa 1 ga watan Mayu. Wannan rangadi na daga cikin kokarin da kungiyar AU take domin kawo karshen yakin da ya barke a Sudan ta Kudu a cikin tsakiyar watan Disamban shekarar 2013, da kuma tabbatar da samun yanayi mai kyau na wanzar da zaman lafiya mai karko a cikin wannan kasa, in ji wata sanarwa ta AU.
Tawagar za ta gana da shugaban kasar Sudan ta Kudu Slava Kiir Mayardit, da ma wasu sauran manyan jami'an gwamnatin kasar. Haka kuma tawagar ta AU za ta shirya wata ganawa tare da tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar dake adawa da shugaba Kiir.
Kwamitin na bincike zai gabatar da wani rahoto cikin watanni uku ga kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar AU. (Maman Ada)