Shugaban kasar Algeriya Abdelaziz Bouteflika, a jiya Talata ya roki masu kada kuri'a a zaben shugaban kasar da su taka gagarumar rawa a zaben wanda ake sa ran gudanarwa a ranar Alhamis, duk kuwa da yake cewa, akwai kiraye-kirayen da ake yi na a kauracewa zaben.
Shugaban kasar Boutflika, wanda ke rike da mulkin kasar ya gabatar da kira a kan daukacin al'ummar kasar da su shiga a dama da su a zaben shugaban kasar da za'a yi.
Boutflika ya kara da cewar, kada kuri'a wani nauyi ne da ya rataya akan 'yan kasar, wanda zai ba su zabin girka 'yancin da suka samu bayan da suka sha wahala sosai.
To amma jam'iyyu da dama a kasar ta Algeriya da kuma wadansu hamshakan mutane, wadanda wasu ke da ra'ayin Islama, wadansu kuwa ke da ra'ayin yaye ra'ayin addini daga al'amurran mulki, na ci gaba da gabatar da kiraye-kiraye na a kauracewa zaben na shugaban kasa, a inda suka yi zargin cewar, hukumomin kasar sun shirya tabka magudi a zaben, domin shugaban kasa dake kan karagar mulkin kasar watau Abdelaziz Boutflika ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulkin kasar a shekaru biyar masu zuwa. (Suwaiba)