Wani bangare na sakamakon kuri'un zaben da aka kada a zaben shugaban kasar Algeriya, ya nuna cewar, shugaban kasar na yanzu Abdelaziz Bouteflika, shi ke kan gaba da kuri'u mafi rinjaye a yankuna da yawa na kasar.
Jaridar kasar da ake kira El Khabar, ta ba da rahoto cewar, Bouteflika ya lashe yawancin kuri'un da aka kada a yankuna da dama kamar su, Msila, Setif, Constantine da Tebessa. Jaridar ta ce, Ali Benflis, mutumin da ake yiwa kallon shi ne babban mai takara na Boutfelika, shi ne ya zo na biyu a yankunan da aka kada kuri'un.
'Yar takara, mace tilo da ta shiga takarar shugaban kasar, Louisa Hanoun da kuma 'dan takara matashi, mafi karancin shekaru, Abdelaziz Belaid, su ne suka zo tsakanin na ukku da na hudu, a inda suka bar Moussa Touati da Fawzi Rebaine a can baya. (Suwaiba)