Ministan harkokin kasashen waje na kasar Algeriya Ramtane Lamamra, ya bayyana cewar, gwamnatin kasar ta sadaukar da kanta wajen ganin ta dauki dukanin matakan da suka dace, na tabbatar da cewar, an gudanar da zaben shugaban kasar ta Algeriya ba tare da samun wani cikas ba. Ana sa ran gudanar da zaben shugaban kasar na Algeriya a ranar 17 ga watan Aprilu.
Ministan harkokin wajen wanda ya yi jawabi ga taron manema labarai a jiya Lahadi, ya ce, wannan mataki da gwamnatin ta dauka, ya nuna cewar, gwamnatin ta Algeriya ta sadaukar da kanta wajen tabbatar da girka tsarin na damokradiyya a Algeriya.
A halin da ake ciki dai gwamnatin ta Algeriya ta gayyaci fiye da masu sa ido a kan zaben har jami'ai 500 daga kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, da kuma kungiyar hadin kan kasashen Afrika, da kungiyar kasashe musulmai, kungiyar tarayyar Turai da MDD.
Hakazalika duk da wadannan dimbin masu sa ido a kan zaben, akwai wasu kungiyoyi na kasar Algeriya guda biyu wadanda su ma za su sa ido a kan zaben, da zummar ganin yadda za'a tafiyar da zaben.
A yanzu haka dai an amincewa mutane guda shidda, ciki har da shugaban kasar Algeriya na yanzu Abdelaziz Bouteflika, daman tsayawa takara zaben na shugaban kasa, a inda kuma tuni aka yi rajista mutane miliyan 22 wadanda ake sa ran za su kada kuri'a a yayin zaben. (Suwaiba)