in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen kudu da hamadar Sahara za su samu ci gaban kaso 6.2 bisa dari a badi
2013-11-01 09:58:58 cri

Asusun ba da lamini na IMF ya yi hasashen cewa, kasashen dake kudu da hamadar Sahara, za su ci gaba da samun habakar tattalin arziki, da kason da ya kai biyar bisa dari a bana, da kuma kaso 6.2 bisa dari a shekarar 2014 mai zuwa.

Wani rahoto da IMF ya fitar a ranar Alhamis, don gane da cigaban da yankin ke samu, ya nuna cewa, ko da yake hakan bai kai ga abin da aka yi hasashe a watan Mayun bara ba, sakamakon sauye-sauyen da kasuwannin hada-hadar kudade da suka fuskanta, da sauran dalilai masu alaka da rashin daidaito a sassan tattalin arziki daban daban, a hannu guda rahoton ya bayyana sashen hakar ma'adanai, a matsayin sashen da zai ci gaba da samar bunkasuwa.

Rahoton ya nuna cewa, wannan sashe zai haifar wa kasashen dake kan gaba wajen fidda ma'adanan, da ma masu karancin kudaden shiga babban ci gaba. Kasashe irin su Kwadebuwa, da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Mozambik da Ruwanda, da kuma Saliyo na cikin irin wadancan kasashe da rahoton na IMF ya bayyana, da cewa, za su ci irin wannan gajiya.

Har ila yau rahoton ya ce, hauhawar farashi zai kasance tsaka-tsaki a bana, yayin da kuma ake sa ran ci gaban raguwarsa a shekara mai zuwa, musamman a kasashe masu samun karancin kudaden shiga.

Da yake karin haske kan wannan batu, darakta a sashen lura da harkokin nahiyar Afirka a asusun na IMF Antoinette Monsio Sayeh, ya ce, babban dalilin ci gaban da kasashen wannan yanki ke samu shi ne, karin zuba jari a fannin ababen more rayuwa, da kuma bunkasar hada-hadar fidda hajoji zuwa ketare. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China