Babbar jam'iyyar hamayya a Mozambique ta amince da ta mika makamanta ga mahukuntan kasar, bayan da aka amince da shigar da mayakanta cikin rundunar soji da sauran hukumomin tsaron kasar.
Wannan mataki da aka cimma a ranar Litinin, bayan doguwar tattaunawa tsakanin wakilan 'yan adawar na Renamo, da kuma na jam'iyyar Frelimo mai mulkin kasar, a cewar sashen gwamnati, babban mataki ne na kwance damar yaki.
Baya ga amincewa da fara mika makaman tun daga ranar Labara 16 ga wata, sassan biyu sun kuma tattauna batutuwan da suka shafi yarjejeniyar baiwa masu sanya ido daga ketare damar lura, da kiyaye dokar haramta kaiwa fararen hula, da dakarun gwamnati hari, musamman a lardin Sofala dake tsakiyar kasar. (Saminu)