Rahotanni daga kasar Mozambique, na cewa, kawo yanzu kimanin mutane miliyan uku ne aka yiwa rajistar kada kuri'a, gabanin babban zaben kasar da ke tafe ran 15 ga watan Oktoba mai zuwa, makwanni biyar da fara rajistar masu zaben.
Rahotanni daga hukumomin shirya zaben kasar sun nuna cewa, akwai kimanin mutane miliyan 9, da suka cancanci kada kuri'unsu yayin zaben kasar. Kaza lika cikin lardunan kasar 10, da babban birnin kasar Maputo, lardin Cabo Delgado dake arewacin kasar ne ke kan gaba, wajen yawan wadanda aka yiwa rajistar da kaso 54 bisa dari, sai Manica mai kaso 39 bisa dari, yayin da lardin Inhambane ke biye da kaso 38 bisa dari.
A cewar kakakin ofishin hukumar gudanar da zaben kasar Lucas Jose, ruwan sama mai karfi, tare da ambaliyar ruwa sun kawowa aikin tarnaki, a tsakiya, da kuma wasu sassan arewacin da kudancin kasar.
A cewarsa, tun daga ranar 17 ga watan nan, aka fara rarraba na'urorin sarrafa hasken rana, domin samar da wutar lantarki, domin ci gaba da gudanar da wannan aiki.
Baya ga yanayin damuna, batun rikicin da dakarun gwamnati ke yi da na 'yan tawayen Renamo, ya sanya wasu daga jami'an aikin kasa fara gudanar da rajistar a wasu yankunan kasar. Babban zaben watan Octobar dake tafe dai shi zai kasance zaben shugaban kasa na 4 a kasar, tun bayan samun 'yancin kanta daga Turawan Portugal a shekarar 1975. (Saminu)