Kasar Ruwanda na fatan kara habaka bangaren samar da kofi da ya samu koma baya yau da kusan shekaru biyu, da ingiza fitar da wannan arzikin noma zuwa dalar Amurka miliyan 157 a shekarar 2017, in ji kwamitin kasa kan cigaba da fitar da albakatun noma (NAEB) a ranar Lahadi.
Shugaban NAEB, mista Corneile Ntakirutimana ya bayyana gaban 'yan jarida tare da nuna cewa, matakan da za'a dauka sun hada da kafa hukumomin siyasa na adalci, fadada filayen noman kofi da kuma shigo da kayayyakin zamani da taki.
Mista Ntakirutimana ya yi wadannan kalamai ne a yayin da aikin noman kofin kasar zai kai wani matsayin shi na ja da baya a wannan shekara, bayan aikin fitar da kofi zuwa kasashen waje ya ragu zuwa dalar Amurka miliyan 60.9 a shekarar bara. Amma jami'in ya bayyana wannan matsala bisa dalilin faduwar farashin kofi a kasuwannin duniya. (Maman Ada)