in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karfin wutar lantarkin Nigeria ya kai Megawatt dubu 4,000
2014-04-24 11:03:54 cri
Ministan makamashin Nigeria Chinedu Nebo yace karfin samar da wutar lantarki a Nigeriya ya karu da fiye da Megawatt dubu 4,000.

A cikin wata sanarwa da ta fito a ranar laraba daga birnin Abuja watau fadar gwamnatin kasar, Ministan makamashin na Nigeriya, yace an samu kaiwa ga wannan nasarar ne saboda katafaren kokarin da ake yi na kawar da lalacewar injuna, tare da bayar da himman da aka yi wajen inganta yadda ake samar da wutar lantarki ga jama'a.

A halin da ake cikin dai karfin wutar lantarkin na Nigera ya karu da Megawatt dubu 4,105.90

Ministan ya jaddada kudurin gwamnati akan alwashin da ta sha na daukar mataki na yaye duk wani cikas na samar da karfin wutar lantarkin da ake bukata.

Ya kuma gabatar da kira akan yan Nigeriya da su yi hakuri tare da nuna fahimta ga kokarin da gwamnatin ke yi tare da bada tabbacin cewar kasuwar wutar lantarki dake kunno kai za ta daidaitu, kuma za'a samu inganci samar da karfin wutar lantarki sannu a hankali. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China