in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kaddamar da sabon shirin tsaro kan iyakokin kasashen Afirka, in ji shugabar Interpol
2013-09-11 10:07:03 cri

Shugabar hukumar 'yan sanda ta duniya, Interpol, Mireille Ballestrazzi, ta ce, nan ba da jimawa ba za a kaddamar da sabon shirin hadin gwiwa na tabbatar da tsaro kan iyakokin kasashen dake nahiyar Afirka, shirin da ake fatan kaddamar da shi zai ba da zarafin yaki da safarar miyagun kwayoyi, da ragowar manyan laifuka da ke addabar nahiyar.

Ballestrazzi wadda ta bayyana hakan ranar Talata 10 ga watan nan, cikin jawabin da ta gabatar gaban mahalarta taro na 22 na hukumar ta Interpol kan Afirka, wanda ya gudana a garin Oran dake wajen Algiers, babban birnin kasar Aljeriya, ta ce, Afirka da nahiyar Asiya, na cikin nahiyoyin da wannan matsala ta fataucin miyagun kwayoyi ke dada habaka.

Karkashin sabon shirin da ake fatan zai samu tallafin sassan jami'an tsaron kasashen da abin ya shafa, Ballestrazzi ta yi amannar cewa, za a kai ga cimma nasarar dakile fataucin kwayoyi, da fasakwaurin hauren giwaye, da kuma safarar muggan makamai.

Daga nan sai ta yabawa kasar Aljeriya, saboda irin hadin kai da take baiwa hukumar ta Interpol, a fagen yaki da laifukan da suka shafi kasa da kasa, tana mai jaddada muhimmancin dake akwai na samun hadin kan 'yan sanda, da jami'an kwastam, da masu tsaron kan iyakokin kasashen Afirka, wajen tabbatar da nasarar wannan sabon tsari.

Taron hukumar ta Interpol karo na 22, ya samu halartar manyan jami'an tsaron Aljeriya, da na hukumar ta Interpol, da wakilin majalissar ministocin cikin gidan kungiyar tarayyar Larabawa, da kuma manyan jami'an hukumomin 'yan sanda daga kasashen Afirka 10. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China