Bankin duniya ya ba da amincewarsa ta zuba kudin kafa fitattun cibiyoyin karatu goma sha tara a cikin manya jami'o'i bakwai na kasashen yammacin Afrika da na tsakiya, bisa dalar Amurka miliyan 150, in ji wata sanarwar wannan hukumar kudi da aka samu a ranar Alhamis a birnin Cotonou.
Cibiyoyin da aka zabe su ta hanyar jarrabawa za su samu kukaden dake da manufar tallafawa azuzuwan da suka fi shahara a fannonin kimiyya da fasaha, kirkire kirkire da lissafi (STIM), da kuma fannin noma da kiwon lafiya, in ji wannan sanarwa.
A cewar kuma wannan majiya, wannan muhimmin shiri na fitattun cibiyoyin karatu a Afrika (CEA) wanda ta hanyar shi daliban nahiyar za su samu kwarewar ilimin kimiyya da fasaha na zamani zai samu tallafin bashin kudi na kungiyar bunkasa cigaban kasa da kasa (IDA) zuwa ga kasashen Afrika takwas. (Maman Ada)