Mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto, ya ce, jami'an tsaron kasar na daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin dakile yunkurin tada hankulan jama'a da 'yan ta'adda ke kokarin aiwatarwa.
Ruto, wanda ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai cocin Likoni dake birnin Mombasa, cocin da wasu mahara suka kaiwa hari ran 23 ga watan nan, suka kuma harbe mutane 6, ya ce, jami'an tsaro sun harbe biyu daga maharan, baya ga guda da ya jikkata yayin wani dauki ba dadi.
Da yake karin haske kan kokarin da jami'an tsaron ke yi don gane da wannan aiki, Ruto ya ce, ko kadan 'yan ta'adda ba za su samu maboya a cikin kasar ba, kuma dakarun gwamnati na zage damtsen kakkabe masu burin tada hankulan al'umma daga birnin na Mombasa, da ma sauran sassan kasar ta Kenya baki daya.
Daga nan sai ya bukaci al'ummar kasar da su ci gaba da gudanar da al'amuransu na yau da kullum yadda ya kamata, yana mai cewa babu wasu 'yan ta'adda dake da ikon hana al'ummar kasar yin hakan.
Bugu da kari mataimakin shugaban kasar yi kira ga al'umma da su sanya ido, wajen kare 'ya'yansu daga shiga kungiyoyin 'yan tada kayar baya, maimakon hakan, a cewarsa, kamata ya yi matasa su mai da hankali ga koyon ilimin da zai amfani kasar baki daya.
Tuni dai aka gurfanar da wasu mutane biyu Abdiaziz Abdullah Abdi, da Isaac Noor Ibrahim gaban kuliya, bisa zarginsu da kasancewa mambobin kungiyar Al-Shabaab, tare da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.
Kenya dai ta fara fama da hare-haren 'yan tada kayar baya masu alaka da kungiyar Al-Qaida ne, tun daga watan Oktobar shekarar 2011, sakamakon zargin da dakarun suka yi mata, na taimakawa wajen yakar su a kudancin kasar Somaliya.
A baya-bayan nan ma mayakan da ke dangantawa da kungiyar Al-Shabaab sun kaddamar da wasu hare-hare a biranen Nairobi, da Mombasa da wasu garuruwa masu makwaftaka da iyakar kasar ta Somaliya, inda suka hallaka mutane da dama. (Saminu)